IQNA

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya amince da Mas'ud  Pezeshkian a matsayin shugaban kasa

16:02 - July 28, 2024
Lambar Labari: 3491596
IQNA - An gudanar da bikin aiwatar da wa'adin mulki karo na 14 a gaban jagoran juyin juya halin Musulunci tare da halartar gungun jami'an gwamnati.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewada misalin karfe 10 na safe a yau Lahadi 28 ga watan Yuli za a gudanar da bikin zartar da hukuncin amincewa da  Massoud Mezkiyan a matsayin shugaban kasa a gaban  jagoran juyin juya halin Musulunci tare da halartar shugaban kasa na rikon kwarya , kakakin majalisa, shugaban bangaren shari'a, shugaban majalisar kwararrun jagoranci, shugaban majalisar fayyace maslahar tsarin musulunci, jami’an Tsaro da gungun jami'ai da wakilai na gwamnati da jakadun kasashen waje.

 

A farkon wannan biki, bayan buga taken jamhuriyar Musulunci, Ahmad Abul Qasimi, makarancin kasa da kasa ya karanta ayoyi daga kur’ani.

Nassin hukuncin shine kamar haka:

Da sunan Allah mai rahma mai jinkai

Godiya ta tabbata ga Ubangiji Masani kuma mabuwayi, wanda ya sake sanya Iran ta Musulunci abin alfahari,  An kammala gagarumin gwajin zaben shugaban kasa da kokarin al'umma da jami'ai, cikin mawuyacin hali, cikin natsuwa  kuma zababbun al'ummar kasa a shirye suke su sauke nauyi mai girma.

Zaben shugaban kasa karo na 14, bayan wa'adin marigayi shugaban kasar da  ba a kammala ba, yana daya daga cikin daukakar al'ummar Iran, kuma wata alama ce ta tabbatar da tsayayyen tsarin Musulunci, kuma yana nuni da hankali da nutsuwa ta yanayin siyasar kasar. Duba da wasu abubuwa marasa dadi a wasu irin wadannan gwaje-gwajen da aka yi a wasu yankuna na duniya na nuni da irin shaharar Iran da Iraniyawa.

A yanzu ina godiya ga daukacin wadanda suka taka rawa wajen samar da wannan karamci, na amince da kuri’arsu ga haziki, mai gaskiya, da farin jini, kuma malami  Dr. Masoud Pezeshkian a matsayin shugaban kasa na Jamhuriyar Musulunci na nada Iran. Kuma tare da addu'o'i da fatan samun nasara, ina tunatar da ku cewa kuri'ar al'umma  za su ci gaba da wanzuwa matukar dai an ci gaba da tsare manufofin bin tafarkin Musulunci da juyin juya hali.

Wassalamu alaikum

Sayyid Ali Khamenei

28 – 7 - 2024

 

4228219

 

 

 

captcha